Daidaita Dangantaka Tsakanin Larabawa Da Isra’ila Barazana Ce Ga Falasdinawa.
Kakakin kungiyar Jihadil Islami Davood Shahab ya fadi cewa Daidaita dangantaka tsakanin wasu kasashen larabawa da ke yankin tekun fasha da Isra’ila barazana ce ga Alummar falasdinu da ma dukkan kasashen larabawa da na musulmi.
Wannan yana zuwa ne bayan da a yan kwanakin nan yarima mai jiran gado na kasar Saudiya Mohammad Bin Salman ya shaidawa mujallar Atlantic Magazine cewa Saudiya ba ta kallon Isra’ila a matsayin abokiyar gaba. Wanda wannan matakin ya harzuka kungiyoyin gwagwarmaya na falasdinu.
READ MORE: Menene bayan amincewar tsibirin Tiran da Sanafir ga Isra’ila!!
A hirar da yayi da gidan talabijin din Press TV Davood shahab ya bayyana daidaita hulda da Isra’ila a matsayin cin Amanar falasdinawa larabawa da alummar musulmi
Daga karshe ya nuna cewa ba mu amince da duk wata kulla hulda da gwamnatin mamaya ba , domin kasancewar Isara’ila a yankin falasdinu baya bisa doka.