Ma’aikatar harkokin addinin Musulunci na kasar Saudiyya a ranar Lahadi ta bayar da sabbin umurni game da amfani da na’urar amsa kuwa watau Sifika na waje a masallatai daga yanzu.
A sabon umurnin da ma’aikatar ta bada, daga yanzu kira Sallah da Iqamah kadai za’a iya amfani da Sifikun waje.
Wannan sabuwar doka ta game dukkan Masallatan Khamsu-Salawaati na masarautar amma an togaciye Masallatan Juma’ah da Masallacin Makkah da Madina, rahoton Haramain Sharifain.
A baya, ana Sallolin farilla biyar da wasu Salloli da Sifiku a bayyane a Masallatan Saudiyya. Amma daga yanzu, za’a yi kiran Sallah da Sifikun waje sannan a yi ainihin Sallah da sifikun cikin Masallatai kadai.
Daga yanzu, an hana Sallah da na’urar amsa kuwa a Saudiyya illa kira da Iqamah A riwayar BBC, an nakalto kalaman ministan harakokin addini na ƙasar Abdul Latif Al Sheikh na cewa duk wanda ya saɓa wannan sabon umurni zai fuskanci fushin hukuma.
Ma’aikatar ta ce manyan malamai irinsu Sheikh Salih bin Fawzan al-Fawzan da marigayi Sheikh Muhammad bin Salih al-Uthaymin sun bayar da fatawa da ya karfafa wannan qadiyya.
Duk da haka, wasu Musulmai a fadin duniya na sukan wannan mataki da gwamnatin Saudiyya ta dauka inda wasu suka soki Yarima mai jiran gado, Muhammad bin Salman.
Daga kafuwar daular saudiyya zuwa yau an shedi tsauraran ra’aypyi na addini sakamakon gina masarautar kasar da akayi bisa akidar wahabiyanci.
Bayan zuwan yarima muhammad bin salman ya fara kokwawar yakar wasu daga cikin akidojin wahabiyancin amma sai dai kuma ya shahada da daukan nauyin ta’addanci da kashe kashen mutane a fadin duniya kama daga gabas ta tsakiya ar zuwa nahiyar afrika.
Masarautar saudiyya tana da hannu dumu dumu a kisan kiyashin ‘yan shi’a fiye da dubu a zariya, tare da batar da dubunnai inda aka tsare da dama karkashin tasirin kungiyoyin ta’addanci na wahabiyya irin su Izala.