Daga cikin dalilan da Imam Hussaini (S.a) ya bayar kan fitowar sa daga birinin manzon Allah (S.a) zuwa makkah inda daga nan ya wuce kufa wanda sojojin yazidu la’anannae suka tare shi a karbala kuma suka aikata abinda suka aikata na kisan sahabban, sa iyalan a karshe shi kansa ma suka kashe shi, daga cikin dalilan wannan fitowa ta imam hussaini s.a kamar yadda aka rawaito Imam Hussaini (S.a) yana cewa ”Ban fito domin girman kai, neman duniya ko neman mulki ba illah na fito ne domin gyara a al’ummar kaka na”.
Wannan yana fito mana da wata babbar natija daga cikin natijojin fitowar Imam Hussain S.a, hakan yana nuna cewa hasali imam s.a ya fito domin ceto addinin kakan sa rugujewa a hannun yazudu dann mu’awiyya wanda a wannan lokacin ake masa kallon halifan musulmi kuma duk abinda ya aiwatar ya zama hujja a tsakanin al’umma, hakan tasa imam hussain s.a, a matsayin sa na jikan manzon Allah kuma imamin zamanin sa ya zabi ya tari gaban yazidu domin nunawa duniya cewa abinda yazidu ke aikatawa fa ba shine asalin sakon addinin musulunci ba.
Wa ya sani da ace Imam Hussain (S.A) baiyi wannan aiki ba yanzu ba mamaki shan gida da wasa da karnuka da zinace zinace sun zama abubuwa masu kyau a addinin msulunci.
Eh mana wani zaiyi mamaki amma idan ka lura zaka ga cewa a wannan lokacin ana kallon yazidu ne a matsayin halifan musulunci kuma duk abinda yayi hujja ne saboda haka tunda yazidu l.a yana shan gida kuma yana wasa da karnuka, kamar yaddaya shahara da zinace zinace, to tana iya yiwuwa da wucewar tsawon zamani al’ummar musulmi ta dauka duk wadannan halaye abubuwa ne masu kyau kamar yadda muke ganin yadda tsahon zamani da rashin daukan matakai ya sanya aka canja addinin kiristanci ya zamana yanzu abubuwa da dama da kiristoci sukeyi a gaskiyar lamari addainin su bai halarta musu ba amma saboda waccan matsalar da aka samu yanzu basa ganin komi a aikata irin wadancan halaye.