Da Zarar Amukra Ta Amince, Za A Kulla Yarjejeniyar Nukiliya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzaedh ne ya bayyana hakan a yau Litinin, yana mai kara da cewa; matakan da Biden yake dauka dangane da batun yarjejeniyar Nukiliya din ba su da dabnbanci da wadanda Trump ya rika dauka a baya.
Kakakin ma’aitar harkokin wajen ta Iran ya kuma ce; A kowace rana Amurka tana fito da wani sabon batu wanda yake cin karo da manufar tattaunawar,saboda a zabtonta za ta kashewa Iran gwiwa.
A 2018 ne dai Amurkan ta janye daga cikin yarjejeniyar Nukiliyar Iran, da halin yanzu kuma take jan kafa wajen kokarin kamawa.