Hukumar Lafiya ta Duniya tace Cutar kyanda da ta barke a Afganistan ta kashe mutane 150 cikin wata tare da kama dubun dubatar mutane, tana mai gargadin adadin mace-macen na iya karuwa.
Kakakin hukumar ta WHO Christian Lindmeier ya shaida wa manema labarai a Geneva cewa, “An samu karuwar masu kamuwa da cutar ta kyanda a dukkannin larduna tun daga karshen watan Yulin shekarar 2021.”
Lindmerer yace daga watan Janairu, cutar ta kama sama da mutum 35,319, ciki har da 3,000 da aka tabbatar a dakin gwaje-gwajen kimiyya, yayin da 156 suka mutu.
Kashi 91 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar da kuma kashi 97 na wadanda suka mutu yara ne ‘yan kasa da shekaru biyar.
A wani labarin na daban Kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa Red Cross ta yi gargadin cewa tsarin kiwon lafiyar kasar Afghanistan yana gaf da durkushewa, sakamakon rufe cibiyoyin kiwon lafiya fiye da dubu 2,000 a duk fadin kasar da ke fama da rikici.
Daraktan kungiyar a yankin Asiya da Pacific, Alexander Matheou ya ce ma’aikata na iya jure aiki ba tare da albashi ba na ‘yan makwanni, to amma da zarar magunguna sun kare babu wani taimakon da za a iya bayarwa ga mara lafiya.
Kungiyar ta ce fiye da ma’aikatan lafiya dubu 20 ne suka daina aiki, ko kuma su ke aiki ba tare da albashi ba, kuma dubu 7 daga cikinsu mata ne.
Ko a makon da ya gabata, sai da hukumar lafiya ta duniya ta yi kashedin cewa kasa da rabin asibitocin da ke Afghanistan ne ke aiki, kuma hakan zai iya kawo cikas a yakin da ka da annobar Corona.
Bayan yaki da ta yi fama da shi na kusan shekaru 20, tattalin arzikin Afghanistan ya samu nakasu tun bayan da kungiyar Taliban ta dare karagar mulkin kasar a watan da ya gabata a tsakankanin takunkumai da kuma dakile taimakon da ke isa kasar daga waje.