Mujallar Fobes ta rawaito cewa, Cristiano Ronaldo na Manchester United ya yi wa Lionel Messi na PSG fintikau, inda a yanzu ya dare duk wani dan wasan kwallon kafa a duniya wajen samun albashi mafi tsoka.
Cristiano Ronaldo zai samu jumullar Dala miliyan 125 kafin fitar da kudaden haraji kenan a cikinn wannan kaka ta 2021-2022.
Dan wasan zai samu Dala miliyan 70 daga albashinsa da kuma kudaden alawus-alawus da Manchester United za ta ba shi.
Sauran kudaden za su fito ne daga kamfanonin da dan wasan ke yi musu tallace-tallace kamar Nike da Herbalife da sauransu.
Mujallar ta Forbes ta ce, Cristiano Ronaldo na cikin sharaharrun ‘yan wasa a duniya, inda yake da mabiya fiye da miliyan 500 a shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram da kuma Twitter.
Hukumar UEFA ta sanar da linka kudin kyautar da za ta bai wa tawagogi 16 da za su taka leda a gasar cin kofin EURO 2022 ta mata.
Sanarwar da UEFA ta fitar game da karin kudaden da masu halartar gasar za su samu, ta ce kasashe 16 za su raba kudin da yawansa ya kai yuro miliyan 16 sabanin yuro miliya 8 da suka karba a shekarar 2017.
Matakin a cewar UEFA kokari ne na kara yawan kudin da ake kashewa gasar ta mata don gogayya da makamanciyarta ta Maza da ta gabata cikin watan Yuni zuwa Yuli.
Haka zalika UEFA ta kuma sanar da ware yuro miliyan 4 da rabi ga kungiyoyin Turai da suka amince da sakin ‘yan wasansu don halartar gasar.
Akalla tikitin kallon wasan dubu 700 za a sayar a wannan karo duk dai a kokarin kawata gasar ta mata mafi girma a Turai.