Jamhuriyar Demokuradiyar Congo ta zama cikakkiyar mamba a Kungiyar Kasashen Gabashin Afrika ta EAC wadda ke gudanar da hada-hadar kasuwancin bai-daya a tsakanin mambobinta da kuma bai wa al’ummar yankin damar zirga-zirgarsu kai tsaye cikin kasashen yankin.
Shugaban Kungiyar ta EAC kuma shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, shi ne ya sanar da karbar Jamhuriyar Demokuradiyar Congo a matsayin sabuwar mamba, matakin da ya bayyana da wani sabon tarihi.
Yanzu haka wannan kungiya ta kara samun fadin kasa wanda ya taso daga Tekun India har zuwa can Tekun Atlantic, abin da ya sa kasashen kungiyar suka kara samun damar damawa da su a fagen goyayyar kasuwanci a nahiyar Afrika.
Tun dai shekara ta 2000 ne dai, aka kafa wannan kungiyar, inda ta yi aiki tukuru wajen karfafa hada-hadar kasuwanci ta hanyar cire kudaden fito a tsakanin mambobinta, yayin da a shekara ta 2010, ta assasa kasuwancin bai-daya.
Yanzu haka Jamhuriyar Demokuradiyar Congo mai yawan al’umma miliyan 90 wadda kuma ke da arzikin karkashin kasa, za ta fadada kasuwancin kungiyar zuwa kusan na mutane miliyan 300.