Kungiyar Kwallon Kafa ta Watford ta kulla kwantiragi da Claudio Ranieri na Italiya domin jagorantar kungiyar a matsayin kocinta
Claudio Ranieri ya kulla kwantiragin shekaru biyu da Watford kamar yadda sanarwar da kungiyar ta fitar ke cewa.
A karkashin jagorancin tsohon kocinta, Watford ta samu maki 7 kacal daga wasanni bakwai da ta buga a gasar firimiyar Ingila a cikin wannan kaka, yayin da take matsayi na 14 a teburi.
Ranieri ya taba lashe kofin firimiyar Ingila tare da Leicester City a kakar 2015 zuwa 2016, sannan ya horas da Chelsea da Fulham, abin da ya sa ake gnin yana da kwarewar da ake bukata.
A wani labarin na daban kylian Mbappe ya ce, da kansa ya nemi ya raba gari da PSG a daidai lokacin da Real Madrid ke marmarin sa a cikin wannan kaka, duk da dai ya nanata cewa, yana jin dadin zamansa a birnin Paris.
Real Madrid ta yi tayin dan wasan mai shekaru 22 akan farashin Pam miliyan 137 a matakin farko amma PSG ta yi watsi da farashin, yayin da ta sake yunkurawa, ita ma PSG din ta sake watsi da farashin.
Dan wasan ya ce, yana son komawa Real Madrid domin kauce wa tsarin nan na raba gari da PSG kyauta bayan karewar kwantiraginsa a kaka mai zuwa.
A cewar Mbappe yana son PSG din ta samu kudi mai tsoka domin sayo wani kwararren dan wasa da zai maye gurbinsa.
Dan wasan ya ce, matsayarsa a bayyane take game da barin PSG.
Matashin dan wasan ya ci wa PSG kwallaye 136 a wasanni 182 da ya buga wa kungiyar tun bayan da ta sayo shi a shekarar 2017 daga Monaco.