China za ta aike da magunguna zuwa asibitocin karkara a ƙasar
Hukumomi a China sun ce za su aike da kayan aiki da magunguna zuwa asibitocin da ke yankunan karkara a ƙasar, a daidai lokacin da ake fargabar za a samu ƙaruwar cutar korona a kasar.
Hukumar lafiya ta yankin ta ce yawancin mazauna karkara ba a yi musu riga-kafin cutar korona ba.
Tuni wasu ƙasashe suka fara ɗaukar mataki mai tsauri kan waɗanda suka shigo ƙasar daga China.
Mai magana da ma’aikatar harkokin wajen China Mao Ning ta ce bai kamata a siyasantar da batun ba.
Ta ce ”a kodayaushe China ta amince ƙasashe su ɗauki matakin kariya daga korona amma ta fannin kimiyya, ta amfanin da hanyoyin da suka dace, kada abin ya zama makarkashiyar siyasa”.
Wasu rahotanni na cewa yawancin biranen da attajiran ƙasar ke ciki, ba su daɗe da farfaɗowa daga zagayen farko na ɓarkewar korona a China ba.
Read More :
Shugabar Tanzania ta dage hanin yakin neman zabe.
‘Yan Najeriya na kokawa kan karancin sababbin takardun kudin da gwamnati ta kaddamar.
Boka ya Yanke Jiki ya Fadi Yayin da Yake ‘Shagalinsa’ da Matar Fast.
Kotu Ta Raba Ango da Amarya Watanni Kalilan Bayan Daura Masu Aur.