China ta zargi Amurka da zuba Ido game da yadda kasar Isra’ila ke barin wuta kan Falasdinawa, bayan da Amurkan ta dakatar da taron kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da zai tattauna a game da shawo kan matsalar.
A cewar China fakewar da Amurka ta yi da rikicn Falasdinawa da yahudawa na hana taron kwamitin tsaro, ya nuna karara yadda take maraba da rikicin, kasancewar in har tana da sha’awar kawo karshen shi babu yadda za’a yi ta dage zaman kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya.
Ma’aikatar harkokin wajen China ta bakin jami’ar yada labaranta Hua Chunying ta shaida wa manema labarai cewa tun lokacin da rikicin ya barke China ke ta kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki matakin gaggawa kan rikicin Falasdinawan da Yahudawa.
China ta ce alamu sun nuna karara, Amurka na da sha’awa kan rikicin Falasdinawan, la’akari da yadda ta nade hannayenta, amma da yake tana da wata bakar aniya kan china ta yi ta tada jijiyoyin wuya kan rikicin al’ummar Uighur.
A wani labarin na daban kuma masu aikin ceto a kasar China na can suna kokarin kubutar da wasu ma’aikatan 21 da suka makale a wata mahakar kwal a yankin Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar, bayan ambaliyar da ta yanke wutar lantarki a karkashin kasa tare da katse hanyoyin sadarwa.
Hatsarin ya faru ne a mahakar kwal ta Fengyuan da ke gundumar Hutubi a yammacin ranar Asabar, lokacin da ma’aikata ke gudanar da ayyukan inganta aikin a wurin, acewar kamfanin dillacin labarai na Xinhua.
Rahotanni sunce, an samu nasarar kubutar da takwas daga cikin ma’aikata 29 da ke mahakar.
A watan Janairu, ma’aikata 22 sun makale a wata mahakar ma’adinai a lardin Shandong da ke gabashin China bayan fashewar wani abu ya lalata hanyar shiga, lamarin da ya sa ma’aikatan suka makale a karkashin kasa na kimanin makonni biyu.