China ta gargadi Amurka game da tsoma baki a dangantakar da ke tsakaninta da India.
Ma’aikatar tsaron Amurka ta bayyana a cikin wata takarda cewa, gwamnatin Beijing ta gargadi Washington da kada ta yi kokarin tsoma baki a cikin alakar da ke tsakanin kasashen biyu bisa zargin rikicin kan iyaka tsakanin Sin da India a shekarar 2020.
“A yayin wadannan fadace-fadacen, jami’an kasar Sin sun yi kokarin yin watsi da tsananin rikicin, da jaddada muradin Beijing na kiyaye zaman lafiyar kan iyaka, da hana wadannan rikice-rikice daga lalata sauran bangarorin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu,” in ji Pentagon.
“Kasar Sin na kokarin hana tashe-tashen hankulan kan iyaka kusantar India da Amurka,” in ji takardar.
Jami’an kasar Sin sun kuma gargadi takwarorinsu na Amurka da kada su tsoma baki cikin alakar China da India.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yayin wani taron manema labarai ba tare da ya yi ishara da wannan rahoton ba, yana mai cewa: atisayen soja na hadin gwiwa tsakanin India da Amurka a wannan watan bai da nisa da kan iyakokin kasar Sin, kuma wannan batu ba shi da wata fa’ida.
don amincewa tsakanin China da India.”
Read More :
Hukumar kwallon kafa ta Sahayoniya: Gasar cin kofin duniya ta tabbatar mana cewa ana kyamar mu.