Wani jirgin fasinja na kamfanin Chine Eastern dauke da fasinjoji 132 ya yi hadari a litinin din nan, wanda hukumar kulada zirga-zirgar sufirin jiragen saman kasar tace, jirgin kirar Boeing 737 ya taso ne daga birin Kunming inda ya nufi kudancin Guangzhou dake kasar china.
Faruwar lamarin dai ta ja hankalin al’umma ciki harda shugaba Xi Jinping wanda ya bayyana kaduwar sa da kuma bada umarnin gudanar da bincike nan ta ke.
Hukumomin kamfani sifirin kasar China sun tabbatar da faruwar lamarin, sai dai basu bada alkaluman adadin wadanda suka mutu ko kuma suka kubuta daga hadarin ba.
Tuni dai kamfanin ya mika sakon ta’aziyar sa ga iyalan fasinjojin da kuma ma’aikatan sa da hadarin ya rutsa da su.
Rabon da a samu mummunar hadarin jirgin sama a China tun a shekarar 2010 wanda ya yi sanadiyar mutumar mutane 42 daga cikin fasinjoji 92 da ke cikin jirgin.
A tarin China, mummumar hadarin jirgin da ya afku a kasar shine na kamfani Northwest a shekarar 1994 wanda dukkanin fasinjoji 160 da ke ciki suka mutu.
A wani labarin na daban Masu binciken hatsarin Jirgin Malaysia Samfurin MH17 da ya kashe mutane kusan 300 sun fito da sakamakon bincikensu na Karshe, inda suka tabbatar da cewa harbo jirgin aka yi daga gabashin Ukraine da Makami mai Linzami BUK da Rasha ke kerawa.
Shugaban Tawagar Masu binciken daga kasar Nerthaland Tjibbe Joustra ya ce mafi yawan tarkacen Jirgin Samfurin MH17 an tsinto su ne a kauyuka da dama da suka hada da Grabove, Rozsypne da Ptropavlivka da ‘yan tawayen ukraine suka fi yawa.
Bincike ya kuma tabbatar da cewar an harba makamin mai linzami ne daga nisa kilomita 320 daga gabashin Ukraine.
Malaysia dai ta sha alwashin shigar da karar wadan da ke da alhakin rikitowar wannan jirgi.
Rasha dai ta bayyana shakun ta dangane da wannan Sakamako.