A cewar Marta Herrera, shugaban sashin yaki da cin hanci da rashawa a ofishin mai gabatar da kara na gwamnatin ta Chile, Babban Lauya Jorge Abbott ne ya fara binciken bayan bayanan Pandora sun bayyana sayar da kamfanin hakar ma’adinai na Dominga da wani kamfani “mai alaka da dangin shugaba Pinera,”
Shugaba Pinera dai ya yi watsi da zargin yana mai cewa tuni aka wanke shi daga duk wani laifi a binciken shekarar 2017.
Batun sayar da kamfanin ma’adinan ga ɗaya daga cikin manyan abokan Pinera ya fara ne tun a shekarar 2010, a lokacin shugabancin sa na baya.
A wani labarin na daban dubban mutane ne suka fito a jiya juma’a a wata gaggarumar zanga-zang da ta gudana a Santiago Chili na kasar ta Chili tareda neman Shugaban kasar Sebastien Pinera ya sauka daga mukamin Shugabancin kasar.
Jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa kwala da ruwan zafi wajen tarwatsa masu bore, da suka sha alwashi ci gaba da gwagwarmaya har sai Shugaban ya sauka daga madafan ikon kasar ta Chili.