Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar sin watau chana ya bukaci amurka da dauki nauyin duk wani aiki na sake gina kasar afghanistan domin itace ke da alhakin duk wasu matsaloli da suke faruwa a kasar.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen chana din yayi wannan bayani ne a taron kasashe masu huldar kasuwanci na nahiyar asiya wanda aka gudanar a birnin dushambe na kasar tajekistan.
Taron wanda ya samu halartar shugannin kasashen Iran, Russia, Chana, India da dai sauran su ya tabo bangarori da dama ciki har da yadda kasashen da nahiyar asiya zasu samar da hanyoyin cigaban juna ba tare da lura da kasashen yammacin turai ba.
Mai magana da yawun ma’aikatar wajen chana ya tabbatar da cewa fitar gaggawa da amurkan tayi daga afghanistan shine ya sabbaba duk wasu matsaloli da ake ciki a kasar ta afghanistan saboda haka dole amurkan ta dauki nauyin duk abubuwan dake faruwa a yanzu.
Wang ya kara da cewa har yanzu ba’a san alkiblar siyasar cikin gidan afghanistan ba, domin a kwai bambance bambancen akida, kabilu da kluma mahangar siyasa saboda haka ba wanda zai iya hasashen abinda ka iya faruwa zuwa nan gaba.
Wang ya cigaba da cewa dole ne wadannan kasashe guda hudu wadanda suka hada da Iran, Chana, Pakistan da kuma Rasha su sanya matsin lamba ga amurkan domin su tabbatar da dauki nauyin samar da tallafin dana damtaka dana tattalin arziki domin dawo da lamurra cikin yanayi mai kyau a afghanistan din kuma ya tabbatar da cewa kin tabbatar da hakan babban kusukure ne wanda zaiyi wuyar gyaruwa zuwa gaba.
Amurka dai tayi fitar sauri daga afghanistan wanda ba wanda yayi hasashen irin hakan daga amurka wanda hakan ya bama taliban damar karbe iko da kudan dukkan iyakokoin ksar ta afghanistan.
Tsohon shugaban kasar afghanistan ashran gani ya sauka daga kujerar sa inda ya fita aya bar kasar ranar 15 ga watan agusta wanda hakan ya bama taliban daman shiga babban birnin kabul ba tare da fuskantar kowacce irin barazana ba.