Shugaban Tunisia Kais Saied ya kori Ministan Harkokin Addini Ibrahim Chaibi daga muƙaminsa bayan gomman Mahajjata sun rasu a yayin Aikin Hajji.
A wata sanarwa da Fadar Shugaban Tunisia ta fitar, ba ta bayyana ainahin dalilin sallamarsa ba, sai dai korar na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu mutuwar Alhazan ƙasar 49 a Saudiyya.
Chaibi a ranar Juma’a kafin korarsa ya sanar da cewa akasarin ‘yan Tunisia da suka mutu sun tafi Saudiyya ne da bizar yawon buɗe ido ba ta shirin Aikin Hajji na ƙasar ba.
An ta caccakar Chaibi a kafafen sada zumunta inda ake zarginsa da wallafa hotunan sa yana Aikin Hajji a daidai lokacin da Alhazan ƙasar ke mutuwa.
A wani labarin na daban Idris ya bayyana yiwuwar aikin zai taimaka wa harkar noma sosai a Arewacin Nijeriya.
Bugu da ƙari, ya yi nuni da irin tasirin da irin waɗannan ayyuka ke yi a faɗin ƙasar nan, inda ya ce a watan da ya gabata an ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan samar da gas guda uku a yankin Neja Delta.
Ya ƙara da cewa aikin na AKK zai tallafa wa Shirin Shugaban Ƙasa na Gas (Pi-CNG), wanda tuni ya jawo jarin sama da dalar Amurka miliyan 50.
DUBA NAN: Kotu Zata Cigaba Da Sauraron Karar Neman Hana Ganduje Bayyana Kansa A Shugaban Jam’iyyar APC
Ya ce, “Aikin bututun na AKK wani ginshiƙin fata ne, wanda zai farfaɗo da tattalin arzikin dukkan ‘yan Nijeriya.”