Kungiyoyin ‘yan tawayen kasar Chadi sun yi kira da a gaggauta sako gungun ‘yan adawar da aka kama a farkon wannan wata sakamakon zanga-zangar kin jinin Faransa.
Kungiyoyin ‘yan tawayen sun yi kira da a gaggauta sakinsu ba tare da wani sharadi ba a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar.
A ranar litinin, da ta gabata hukumomin Chadi sun tuhumi wasu jiga-jigan jam’iyyar adawa ta Wakit Tamma da laifin cin zarafin jama’a sakamakon zanga-zangar da suka shirya ranar 14 ga watan Mayu wanda ta kaiga tsare su.
An tsare kodinetan Wakit Tamma, Max Loalngar, kuma an gurfanar da shi a gaban kotu a ranar Alhamis, saidai an dage sauraron shari’ar nasu har zuwa ranar 6 ga watan Yuni.
Zanga-zangar ta shafi Faransa ne, wadda masu fafutuka ke zargin tana goyon bayan gwamnatin mulkin soja a Chadi.
A wani labarin na daban daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga zanga Asabar a N’Djamena, babban birnin kasar Chadi dangane da abin da suka kira kasancewar Faransa a kasar, wadda suka zarga da taimaka wa sojojin da ke mulkin kasar.
Masu zanga zangar sun kona akalla tutocin tsohuwar uwargijiyar tasu 2, kana suka lalata gidajen mai mallakin kamfanin Total na kasar Faransa, tare da yin awon gaba da wasu kayayyaki a gidajen man.
Zanga zangar da kungiyar farar hular nan ta Wakit Tamma mai hamayya da gwamnatin kasar ta shirya ta samu goyon bayan hukumomi da alama, inda kamfanin dillancin labaran Faransa ta ruwaito cewa ana iya ganin tawagar ‘yan sanda mai karfi da ke tabbatar da cewa ba a wuce gona da iri ba.
A ranar 20 ga watan Afrilu shekarar 2021 ne rundunar sojin kasar Chadi ta sanar da cewa shugaba Idriss Deby Itno ya mutu a fagen daga, yayin fafatawa da ‘yan tawaye, inda a ranar ce aka nada dansa Mahamat Deby a matsayin shugaban kasar.