Rahotannni sun tabbatar da canje canje a tsarin dokokin Isra’ila wanda hakan zai rage karfin fada ajin bangaren hukumar shari’a a tsarin gudanarawar kasar.
Kamar yadda kafar sadarwa ta kasa da kasa mai suna Tasnim ta rawaito, kunshin dokar rage karfin fada ajin bangaren shari’a din a ranar litinin ya samu wucewa da kuri’u 64, kuma ba tare da wani ra’ayi da ya kalubalanci wannan kuduri ba.
Kamar yadda rahotannni suka zo, masu adawa da wannan kunshin kuduri na canje canje ba su halarci wannan zama ba.
Tabbatar da wannan kuduri mataki ne na farko domin share fagen rage ikon bangaren hukuma shari’a kasar ta Isra’ila.
Da tabbatar da wannan kuduri kuma yanzu bangaren hukumar shari’a na kasar ba shi da ikon hana wani mataki da gwamnati zata dauki bisa amfani da dabarar yayi hannun riga da hankali.
A halin yanzu daya daga cikin rukunan dokoki a kasar shine, sanya idon bangaren shari’a a kan kudurorin majalisa da kuma gwamnati bisa ma’aunin hankali.
Ta yadda alkalai 15 zamu duka dokoki gami da umarni kuma ta tabbatar ba su fita daga da’irar hankali da sanin ya kamata ba kuma idan suka ga ba su cika wadannan ka’idoji ba, suna da ikon hana tabbatar da su.