Kasar Canada tace zata aike da kayan agaji na Dala miliyan 25 domin taimakawa Falasdinawan dake Gaza da Gabar Yamma da Kogin Jordan mako guda bayan kawo karshen tashin hankalin da aka yi tsakanin su da Isra’ila wanda yayi sanadiyar rasa dimbin rayuka.
Ministan harkokin wajen kasar Canada Marc Garneau yace za’a mika agajin ga Majalisar Dinkin Duniwa wanda ya kunshi Dala miliyan 10 domin samar da abinci da ruwan sha da kuma gyara gidajen da suka rushe, yayin da kuma za’ayi amfani da Dala miliyan 10 wajen samar da magunguna da kuma kayan more rayuwa.
Sanarwar gwamnatin Canada tace za’ayi amfani da Dala miliyan 5 wajen aikin gina zaman lafiya da zummar ganin an samu kwanciyar hankali a Yankin Gabas ta Tsakiya baki daya.
Akalla Falasdinawa 254 suka mutu a rikicin da aka kwashe kwanaki 11 anayi, yayin da Israila tayi asarar soja guda da fararen hula guda 12.
A wani labarin kuma yahudawan Isra’ila sun kashe wasu Falasdinawa guda hudu bayan sun yi kokarin abka masu a yamma da kogin Jordan.A makon da ya gabata rikici ya barke tsakanin Falasdinawa da Sojojin Isra’ila a birnin Hebron da ke yankin yamma da Kogin Jordan, a yayin da Falasdinawan suka yi jana’izar ‘yan uwansu matasa biyar da suka rasa rayyukansu a arangama da Jami’an tsaron na Isra’ila.
Wanann dai na zuwa ne bayan yahudawan Isra’ila da ke kula da kan iyaka sun bindige wani Bafalasdine har lahira a wajen binciken ababan hawa, inda suka ce ya yi yunkurin daba wa daya daga cikinsu wuka.
Tun bayan da tarzomar ta fara a watan jiya a birnin Kudus, kawo yanzu Falasdinawa 66 sun rasa rayyukansu, inda Yahudawa suka rasa mutane tara.
Rundunar sojin yahudawan Isra’ila tace Falesdinawan sun yi kokarin dabawa jami’an Sojin wuka, lamarin da ya sa aka harbe su.
Faladdinawa uku ne yahudawan na Isra’ila suka kashe a wata mahada a yankin Gush Etzion kudu da birnin Kudus.