Hukumar kwallon kafar Afrika (CAF) ta ce, ‘yan wasan nahiyar za su iya ci gaba da takawa kungiyoyinsu leda har zuwa nan da ranar 3 ga watan Janairu gabanin komawa kasashensu don fara shirin tunkarar wasannin cin kofin nahiyar na bana.
Sai dai wata wasika da FIFA ta aikewa kungiyoyi ta bayyana musu cewa CAF ta amince da baiwa ‘yan wasan nahiyar damar ci gaba da taka leda har zuwa ranar 3 ga watan Janairu gabanin basu damar tafiya gida.
FIFA wadda ta bayyana matakin na CAF a matsayin girmamawa ga kungiyoyi wadanda yanzu haka ke fuskantar kalubalen sakin ‘yan wasan saboda asarar da hakan za ta haifar musu, bayan tattara karfinsu wajen dogaro da ‘yan wasa Afrikawa.
Matakin CAF na nuna cewa yanzu Liverpool na da damar amfani da Mohamed Salah Sadio Mane da kuma Naby Keita a wasanta na ranar 2 ga watan Janairu da za ta kara da Chelsea wadda ita ma ke da damar amfani da mai tsaron ragarta dan Senegal Edouard Mendy.
Gasar ta cin kofin Afrika da za ta gudana daga ranar 9 ga Janairu zuwa 6 ga Fabarairu na nuna cewa kungiyoyin firimiya ne kan gaba ta fuskar asarar ‘yan wasa da za su taka leda a gasar wanda ya shafi kusan dukkaninsu, in banda Leeds United da Newcastle United da Norwich City da kuma Tottenham wadanda basu da asara.