Burtaniya; Wata Babbar Kotu Ta Amince Da Maida Yan Gudun Hijira Rwanda.
Wata babbar kotu a kasar Burtaniya ta goyi bayan hukuncin wata karamar kotun kasar wanda ya bawa gwamnatin kasar Maida yan gudun hijira zuwa kasar Rwanda.
Kafin haka dai gwamnatin kasar Burtania ta kulla yarjejeniya da gwamnatin kasar Rwanda kan cewa zata maida wasu yan gudun hijira zuwa kasar.
Labarin ya kara da cewa kungiyoyin kare hakkin biladama da dama sun yi alllawadai da wannan shirin na gwamnatin kasar Burtania, suna kuma ganin cewa yin hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.
Hukumar mai kula da yan gudun hijira na MDD UNHCR ta yi allawadai da wannan shirin kuma tana ganin hakan bai dace ba, kuma ya sabawa dokokin kasa d kasa da kasa.
READ MORE : Lebanon Ta nisanta yiwuwar bullar yaki tsakaninta Da Isra’ila kan Rikicin kan iyaka.
Yan gudun hijiran dai sun tsallaka teku ne da kananan jiragen ruwa har suka isa kasar Burtania a cikin yan shekarun da suka gabata. A cikin watan Yuli mai zuwa ne ake saran babban kotun zata yanke hukunci na karshen wannan batun.
READ MORE : Burkina Faso – ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Akalla Mutane 50.
READ MORE : Kotun Senegal Ta Zartas Da Hukuncin Dauri Akan Shugaban ‘Yan Tawayen Casamance.