Gwamnatin Burkina Faso zata dauki karin sojoji dubu uku domin kara karfin sojojin kasar dake fama da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi, da akasari ke kaiwa ga rasa rayukan sojoji da fararen hula.
Kuma za’a zakulo zaratan ne daga jihohin kasar 13.
An yi kiyasanin Burkina Faso na da sojojin tsakanin dubu 15 zuwa 20, kuma akasarinsu sojojin kasa ne, da suka shafe shekaru bakwai suna fafatawa da mayaka masu ikirarin jihadi.
A wani labarin na daban a karon farko tsohon jagoran ‘yan tawayen Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da ake zargi da aikata laifukan yaki da kuma ta ke hakkin bil-Adama Maxime Makom, ya bayyana a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC.
Makom mai shekaru 43, a ranar Litinin ne Chadi ta mika shi ga hukumomin kotun ta ICC da ke birnin Hague a Holland, inda ya tabbatar da cewar an shaida masa lafukan da ake zargin sa da aikatawa.
Lauyan sa ya bayyana cewar, hukumomin Chadi sun azabtar da Makom a tsawon lokacin da ya shafe a hannunsu ta yadda suka rika ciyar da shi lalataccen burodi baya ga barinsa ya kwana a kasa ba gado.
An dai tsaida ranar 31 ga watan Janairun badi domin fara sauraron karar.
Rikicin da ‘yan tawayen Seleka da kuma Balaka suka haifar a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma sanya wasu rasa muhallan su.
Tuni dai aka gurfanar da biyu daga cikin wadanda suka jagoranci tawaye a kasar, Patrice Edouard Ngaissona da kuma Alfred Yekatom a gaban kotun, yayinda aka tsaida watan Satumba don fara shari’ar Mahamat Said Abdel Kani wanda ake zargi a matsayin kwamandan kungiyar Saleka da aikata laifukan yaki.