Akalla mutane 50 ne ‘yan ta’adda suka kashe a arewacin Burkina Faso, al’amari mafi muni tun bayan juyin mulkin da aka yi a kasar, kamar yadda kakakin gwamnatin kasar Lionel Bilgo ya bayyana a Litinin.
Bilgo ya ce ya zuwa yanzu sojoji sun gano gawarwaki 50 bayan da aka kai hari a kauyen Seytenga a cikin daren Asabar, inda ya kara da cewa adadin na iya karuwa.
Ya shaida a wani taron manema labarai cewa ‘yan uwan wadanda abin ya rutsa da su sun koma kauyen, k,um aba mamaki sun tafi da wasu gawarwaki.
A garin Seytenga ne aka yi mummunan bata kashi a makon da ya gabata, inda aka samu sarar rayuka.
An kashe jandarmomi 11 a ranar Alhamis a wannan gari, lamarin da ya wajabta wani sintirin soji da ya yi sandin mutuwar mayaka masu ikirarin jihadi guda 40.
Kungiyoyin agaji a yaankin sun ce kimanin mutane dubu 3 ne aka bai wa mafaka a garuruwan da ke makwaftaka da kauyen.
A wani labarin na daban akalla jandarmomi 11 ne mahara dauke da makamai suka kashe a kauyen Setenga dake lardi Seno na kasar Burkina Faso a wani hari da suka kai marecen jiya alhamis.
Hukumomin tsaron kasar ta Burkina Faso sun tabbatar da wannan sabon harin da mayakan jihadi suka kai wannan yanki a wani lokaci da majalisar soji dake rike da madafan ikon kasar ke fuskantar mantsin lamba daga waje da cikin kasar a sha’anin da ya shafi tsaro da siyasa,musaman a wani lokaci da kungiyar kasashen Ecowas ke fatan samun tabbaci daga majalisar sojin Burkina na sake mika mulki ga farraren hula.
Wannan hari na baya-bayan nan ya yi sanadiyyar mutuwar Jandarmomi 11 a Seytenga,wanda ke nuna karara durkushewar sha’anin tsaro a arewacin kasar duk da kokarin al’uma da suka dau niyar kaffa kungiyar yan sa kai tare da gundumuwar hukumomin Burkina Faso.
Burkina Faso na daga cikin kasashen yankin Sahel da suka hada da Nijar,Mali hata arewacin Jamhuriyar Benin na fuskantar hare-haren mayakan jihadi.