‘Yan bindiga sun sako fursunoni kusan 60 a wani hari da suka kai wani gidan yari a arewa maso yammacin kasar Burkina Faso cikin dare, tare da kona motoci kafin su tsere.
Sanarwar da hukumomin tsaron kasar suka fitar ta ce mutanen dauke da makamai sun shiga garin Nouna ne da tsakar dare a kan motoci da kuma babura, inda suka yi ta harbin kan mai ‘uwa dawabi.
Burkina Faso dai na fama da hare-haren masu jihadi da suka yadu daga makwabciyarta Mali cikin shekaru goma da suka gabata, inda ake kai munanan hare-hare a duk mako.
Abin da bayanai ke cewa shine, an kashe dubban mutane a fadin kasar, kuma an tilasta wa miliyoyin jama’a kauracewa gidajensu, sakamakon hare-haren masu tayar da kayar baya.
Babu wanda ya rasa ransa a harin da aka kai gidan yarin, amma an harbe wani mayakin sa kai a cewar majiyoyin tsaro. An kuma kona motoci da babura da dama, baya ga yin barna a ofisoshin gidan yarin.
Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.
Wannan farmakin ya zo ne sa’o’i kadan bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe akalla mutane 11 a tsakanin garuruwan Dori da Gorgadji da ke arewacin kasar, kuma daga cikin wadanda suka mutu har da ‘yan bindiga 9 da fararen hula biyu.
Rundunar sojin Burkina Faso a ranar Juma’a ta ce an kashe wasu sojoji 11 da ‘yan bindiga da kuma jami’an ‘yan sanda a wasu hare-haren da aka kai a cikin makon da ya gabata, amma sama da ‘yan ta’adda 20 ne aka kashe a wani ramuwar gayya.