Burkina Faso Na Son Ta Amfana Da Kwarewar Iran Wajen Yaki Da Ta’addanci.
Sabuwar ministar harkokon wajen kasar Burkina Faso Olivia Rouamba da aka nada ta bukaci kasar Iran a matsayinta na kasar da ta yi fama da ayyukan ta’addanci na tsawon shekaru da ta yi aiki da kasar Burkina Faso don bata kwarewar da take da shi wajen yaki da Ta’adanci
A yau ne ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Abdollahiyan ya aike da sakon taya murna ga sabuwar ministar harkokin wajen kasar Burkina Faso, Olivia Rouamba na sabon matsayin da aka bata, inda ya yi mata fatar samun Nasara a sabon mukamin da aka bata.
Da yake tsokaci game da muhimmancin da nahiyar Afrika ke da shi a siyasar Harkokin wajen Iran, ya Jaddada aniyar kasar na fadada dangantaka tsakaninta da nahiyar Afrika musamman ma kasar Burkina Faso.
Har ila yau Amir Abdullahian ya bayyana ayyukan da kungiyoyin yan ta’adda na Takfiri da masu tsattsauran ra’ayi suke yi a kasashen yammacin Afrika babban abin damuwa ne.
Ana ta bangaren minsitar harkokin wajen kasar Burkina Fasa bayan ta bayyana aniyar kasa na fadad dangantaka da kasar Iran ta bukaci a bunkasa yin aiki tare tsakaninsu a bangaren kimiya da fasaha da kuma sarun taimako daga kasar Iran