Burkina Faso; Mutane 34 Ne Suka Rasa Rayukansu A wasu hare-Haren Ta’addaci.
Akalla mutane 34 ne aka kashe a Burkina Faso a wasu hare-hare biyu da wasu masu dauke da makamai suka kai a arewa maso yammacin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nakalto Babu Pierre Basinga, gwamnan yankin Boucle de Mohon na cewa, a daren Lahadi-Litinin, mazauna yankunan karkarar Buraso (arewa maso yamma) sun fuskanci wani hari na ‘yan ta’adda masu dauke da makamai,” yana mai bayyana cewa harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 22 tare da jikkata wasu da dama, baya ga asarar dukiya.
Wata majiyar tsaro ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP a safiyar jiya litinin cewa harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 15 maza da mata da kananan yara, bisa ga wani adadi na wucin gadi da aka bayar, yayin da wata majiya mai tushe ta bayyana cewa adadin wadanda suka mutu a harin ya kai 20.
A cewar daya daga cikin mazauna kauyen, ‘yan bindigar sun fara yawo ne da misalin karfe biyar na yamma a kauyen, inda suka rika harbe-harbe a iska, a cikin dare kuma suka dawo suka rika harbin mutanen kauyen. “
Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa, an kai wani mummunan hari a ranar Asabar a Namisegina da ke lardin Yatinga a arewacin kasar.
Majiyar ta ce ” wannan harin ya kai ga mutuwar mutane 12, ciki har da masu aikin sa-kai uku domin kare kasar, Wannan harin ya yi sanadiyyar tserwar dubban mutane daga muhallansu.