Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga lumana jiya asabar a garin Pama dake lardin Kompienga dake gabashin kasar Burkia Faso da nufin nuna takaici da damuwar su ganin ta yada mahara ke ci gaba da afkawa mazauna wadanan yankuna.
Masu zanga-zangar sun samu goyan bayan shugabanin addinai,Sarakunan gargajiya, kungiyoyin farraren hula ,suka kuma yi amfani da wannan dama tareda rubuta wasika ga babban jami’in gwamnati na yankin don nuna masa rashin ko in kula da majalisar soji ke yi dangane da batun tsaro a wannan yaki da yan ta’adda.
Burkina Faso da wasu kasashen yankin Sahel na fama da wannan matsala ta yan ta’adda,al’amarin da ya durkusar da lamuran da suka shafi tattalin arziki,kasuwanci.ilimi da kiwon lafiya ga baki daya.
A wasu yankunan kasar ta Burkina Faso musaman arewacin kasar,sheidu sun tabbatr da cewa jami’an tsaro sun bar wurare ga baki daya ga hannun yan bindiga.
A wani labarin na daban kuma akalla Sojojin biyar da ‘yan ta’adda 30 aka kashe a arewacin Burkina Faso, bayan wani kazamin hari da ake zargi mayaka masu ikirarin jihadi ne suka kai wani sansanin sojin kasar ranar Asabar.
Rundunar sojin Burkina Faso tace da safiyar wannan Asabar ne wani adadi mai yawa na ‘yan ta’adda dauke da manyan makamai suka kai kazamin hari sansanin su dake Bourzanga”, wani yanki a lardin Bam da ke tsakiyar yankin arewa, “inda nan take suka maida martani.
Sanarwar tace, baya ga “Sojoji 5 da suka mutu wasu 10 sun samu raunuka yayin artabun”.
Adadin farko yace, sun yi nasarar kashe ’yan ta’adda aƙalla talatin yayin da saurann sunka rance na kare.