Rundunar sojin Burkina Faso ta ce dakarunta bakwai da kuma wasu ‘yan sa-kai hudu sun rasa rayukansu, yayin harin kwanton bauna har kashi biyu da ‘yan ta’adda suka kai musu a yankin arewacin kasar mai fama da matsalar tsaro.
Sanarwar da rundunar sojin Burkina Fason ta fitar a wannan Juma’a ta ce, an kai harin farko ne a kusa da garin Solle ranar Alhamis din da ta gabata inda sojoji biyu suka mutu da wasu farar hula hudu, ‘yan sa-kai da ke taimaka wa sojojin.
A wani harin na dabam kuma, dakaru biyar ne suka halaka a dai ranar ta Alhamis a garin Ouanobe.
Sanarwar ta kara da cewa, mutane 9 ne suka jikkata, yayin da kuma aka gano gawarwakin maharan kimanin 20 lokacin da jami’an tsaro ke sintiri a wuraren da aka kai farmaki, bayan da suka tarwatsa ‘yan ta’adddan, tare da lalata makamansu da dama da kuma kwace wasu.
Tun daga shekarar 2015, kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS ke kai hare-hare a arewaci da gabashin Burkina Faso, inda suka kashe mutane sama da 2,000 tare da raba kusan miliyan biyu da muhallansu, tashin hankalin da ya shafi sassan Mali da Nijar da ke makwabtaka da kasar.
A wani labarin na daban Amurka ta ce akwai alamun da ke nuna cewar kasar Korea ta Arewa ta mallaki tarin makaman da ba’a san adadin su ba, bayan gwajin wani makami mai linzami mafi girma da Koriyar ke cewa na iya kai wa kasar Amurka.
Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan ya shaidawa manema labarai cewar matakin na Korea wani yunkuri ne na takala, kuma suna tunanin cewar kasar na da tarin makaman da ba su sani ba.
Gwajin da Korea ta gudanar ranar alhamis shi ne irin sa na farko da kasar ta yi a karkashin jagorancin shugaba Kim Jong Un tun daga shekarar 2017.
Kamfanin dillancin labaran Korea ya ruwaito cewar a karkashin sanya idon shugaba Kim aka gwada shu’umin makamin wanda ya ke tabbatar da aniyar kasar na fuskantar duk wata kasa da za ta kalubalance su.
Rahotanni sun ce sabon makamin ya yi tafiyar da ya zarce duk wasu makamai masu linzamin da aka gwada a shekarun baya tare da wani da aka kera na musamman domin kai hari ko ina a cikin Amurka.