Dubban mutane suka gudanar da zanga-zanga a Dori, dake arewacin Burkina Faso, don yin Allah wadai da halin rashin tsaro da kasar ke fuskata bayan kisan akalla mutane 132 a ƙauyen Solhan, wanda suke zarhin mahukunta da sakaci.
Masu zanga-zangar, wadanda suka taru a Dori, babban birnin yankin Sahel, suna rera wakon neman zaman lafiya a Sahel da Burkina Faso baki daya.
A ranakun 4 zuwa 5 na watan Yuni, mahara suka kashe aƙalla mutane 132, a kauyen Solhan dake kusa da kan iyakar kasar da Mali da Nijar, a cewar gwamnati, yayin da majiyoyin yankin sukace adadin wadanda aka kashe ya kai 160.
Hari mafi muni
Wannan harin shi ne mafi muni tun bayan fara rikicin dake da nasaba da mahara masu ikirarin jihadin a Burkina Faso shekaru shida da suka gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 1,400 tare da tilastawa miliyoyin mutane barin gidajensu.
Masu zanga-zangar sun je ofisoshin gwamnan, inda suka mika wata takarda da ke yin kira ga jerin matakan gaggawa na kare lafiyar mazauna da hanyoyi, in ji Yaya Dicko, daya daga cikin wadanda suka shirya taron.
An kiyasata a kalla kusan gabadayan kasashen afirka suna fama da matsalolin tsaro a wannan lokaci , lamarin da ake alakanta shi da kutsen kasashen yammacin turai a kokarin su na satar dukiya daga kasashen na afirka ta hanyar amfani da tashe tashen hankula domin dauke hankalin mutane wanda hakan shine ake tsammanin yana faruwa a kasar ta burkina faso.
Kasashe irin su Najeriya,Mali,Nijar da dai sauran su suna cikin ire iren wannan mummunan hali a yanayi daban daban.