Burhan Ya Gana Da Jami’an MDD Don Farfado Da Tattaunawa Da Yan Adawa.
Shugaban kasar Sudan Abdulfattah Alburhan ya gana da wakilan MDD da kuma kasar Burtaniya a birnin Khartun don farfado da tattaunawan tsakanin gwamnatin sojoji da yake jagoranta da kuma yan siyasa kuma ‘yan adawar kasar.
Jaridar Sudan Tribune ta bayyana cewa a Ranar Alhamis da ta gabata ce Burhan ya gana da wakilay kungiyar tarayyar Turai a yankin gabacin Afirka Annette Weber da kuma Moazzam Malik jakadan kasar Burtania a nahiyar Afirka.
Bangarorin uku sun tattauna batutuwa da dama daga ciki har da shirin kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya wacce zata kammala aikin maida kasar kan turbar Demokradiyya a kasar.
Majiyar fadar shugaban kasa a birnin Khartun ta tabbatar da cewa shugaba Burhan ya gana da wadannan jami’an kasashen yamma kuma maganarsu ta kare a kan kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya.
Ms Weber ta bayyana cewa ta gamsu da shawarar shugaba Burhan na kafa sabuwar gwamnati tare da hadin guiwa da yan siyasar kasar wanda zai bawa kasar Damar dawoda tsarin shugabanci na democradiyya a kasar.
Tun ranar 25 ga watan Octoban da ta gabata ce shugaban Burhan ya jagoranci wani juyin mulki a kasar ta Sudan wanda ya kawo karshen gwamnatin hadaka tsakanin sojoji da ‘yan siyasa, sannan mutanen suka fara zanga-zangar kin jinin gwamnatin sojojin kasar. An kashe mutanen da dama, sannan wasu da dama sun kulle a gidajen yarin kasar.