Bulgariya Ta Kori Jami’an Diflomasiyyar Rasha Guda 70 Daga Kasarta.
Gwamnatin kasar Bulgariya ta sanar da korar jami’an diflomasiyyar Rasha 70, kuma gwamnatin Rasha ta sha alwashin mayar da martani
Gidan talabijin din kasar Bulgariya ya watsa sanarwar fira ministan kasar Kiril Petkov cewa: Gwamnatin Bulgariya ta dauki matakin korar jami’an diflomasiyyar kasar Rasha 70 daga kasar, tana mai da’awar cewa: Ana zarginsu ne da hannu a gudanar da ayyukan leken asiri a kasar ta Bulgariya.
Fira ministan Bulgariya Kiril Petkov ya rubuta a shafinsa na Telegram cewa: Yana taya jami’an tsaron Bulgariya da ma’aikatar harkokin wajen kasar murna kan wannan gagarumin aiki da suka yi, kuma yana sanar da dukkan ‘yan kasashen waje, ba kawai Rasha ba, gwamnatin Bulgariya tana da hukumomi da suke kare masalahar kasar, don haka duk wanda ya yi wani abu da zai shafi masalahar Bulgariya, to lallai za a kore shi daga kasar.
READ MORE : Masar Ta Karyata Batun Cewa; Tana Hana ‘Yan Sudan Shiga Kasarta.
A nata bangaren ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta jaddada cewa: Za ta mayar da martani kan wannan mataki da kasar Bulgariya ta dauka na korar jami’an jakadacinta bisa zargi maras tushe cewa: Suna gudanar da ayyukan leken asiri a kasar.