Babbar Kotun Majalisar Dinkin Duniya ta fara sauraron ƙara ta kwanaki biyu game da bukatar Afirka ta Kudu ta neman kotun ta umarci Isra’ila da ta dakatar da hare-haren soji kan garin Rafah na Kudancin Gaza.
A karo na hudu, Afirka ta Kudu ta bukaci kotun kasa da kasa kan matakan gaggawa tun bayan da kasar ta shigar da karar farko tana zargin Isra’ila da ikata kisan kiyashi a Gaza.
Bukatar baya-bayan nan ta bayyana cewar roƙon da aka yi na farko da matakin da Hague ta dauka bai isar ba wajen magance “Munanan hare-haren soji kan ‘yan gudun hijirar Gaza.”
Isra’ila ta bayyana Rafah a matsayin yankin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa na Hamas, suna watsi da gargadin su kauce wa gargadin Amurka kan nisantar duk wani abu da zai illata fararen hula.
Afirka ta Kudu ta bukaci kotun da ta umarci Isra’ila ta janye daga Rafah; ta dauki matakan tabbatar da jami’an MDD, ma’aitan jinƙai da ‘jaridu sun shiga yankin Gaza, sannan ta ba su rahoto cikin mako guda kan yadda take aiki da wannan bukata.
‘Gwamnatin ‘yan nuna fifikon farar fata’
A watan Janairu, Alkalai sun umarci Isra’ila da ta nisanci kisa, rushe gine-gine da duk wani nau’i na kisan kiyashu a Gaza, amma tawagar alkalan sun dagakar da bayar da umarnin a daina kai hare-haren da suka mayyar da yankunan Falasdinawa kamar bola.
A umarni na biyu a watan Maris, kotun ta ce dole ne Isra’ila ta dauki matakan inganta ayyukan jinƙai a Gaza, ciki har da bude karin hanyoyin kai kayan abinci, ruwa, man fetur da sauran kayayyaki.
Mafi yawan jama’ar Gaza su miliyan 2.3 sun rasa matsugunansu tun bayan fara kai hare-haren Isra’ila.
DUBA NAN: Hukumar Alhazai Ta Bayyana Lokacin Da Za’a Kammala Aikin Hajin Bana
Afirka ta Kudu ce ta fara kai karar a watan Disamban 2023 kuma tana kallon matakin shari’ar ya samo aali dne daga yadda kasar take.