Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan sabuwar dokar karin kudaden haraji ga masu kiran waya a kasar baki daya.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da fadar shugaba Buhari na Najeriyar ta fitar, inda ta ce za’a yi karin kwabo guda kan kowanne kira da dan Najeriya zai yi, kari kan abinda aka saba biya.
Ta cikin sanarwar fadar shugaban Najeriyar ta ce za’a yi amfani da kudaden ne wajen taimakawa gajiyayyu da kuma zuba su don tsamo tattalin arzikin kasar daga mawuyacin halin da yake ciki.
Ko da sanarwar ta ci gaba da karin bayani ta ce za’a fi karkata kudaden ne ga bangaren lafiyar gajiyayyu da masu bukata ta musamman don inganta lafiyar su.
Tuni dai ‘yan Najeriya suka fara yiwa sabuwar dokar bore, a ganin su halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki kamata ya yi a ragewa dan Najeriya harajin da yake biya ba wai kara masa ba.
Gwamnatin Najeriya ta sake tsawaita wa’adin hade layukan waya da lambobin sirrin jikin katin dan aksa wato NIN bayan karewar wa’adin a daren karshe na 2021 wato ranar 31 ga watan Disambar shekarar.
A wani labarin na daban hukumar sanadarwa ta Najeriyar a wata sanarwa da ta fitar sa’o’I kalilan gabanin karewar wa’adin na jiya juma’a ta sanar tsawaita shi zuwa 31 ga watan Maris din shekarar da muka shiga.
Wannan dai shi ne karo na 9 da mahukuntan Najeriyar ke tsawaita wa’adin, sakamakon karancin ‘yan kasar da suka amsa kiran hade layukan nasu da lambobin NIN.
Wata sanarwar hadakar hukumar sadarwa ta Najeriyar NCC da hukumar samar da katin dan kasa NIMC mai dauke da sa hannun Ikechukwu Adinde da Kayode Adegoke ce ta sanar da matakin tsawaita wa’adin zuwa karshen watan Maris.
Sanarwar hadakar ta ruwaito ministan sadarwar Najeriyar Dr Isa Ali Ibrahim Pantami na tabbatar da sahalewar gwamnati wajen tsawaita wa’adin don baiwa ‘yan kasa damar kammala rijistar hade layukan nasu na waya da lambobin na NIN.
Bayanai sun ce har zuwa yanzu ba a iya hade kasha 2 bisa 3 na layukan ‘yan Najeriyar da lambobin na NIN ba duk da yadda hukumar NIMC ta yi ikirarin samar da lambobin na sirri ga mutane miliyan 71 a cibiyoyinta dubu 14 da ke sassan kasar.
Hukumar ta NIMC ta sanar da shirin bude cibiyoyi 31 a ketare da fara hade layukan ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje da lambobin na NIN nan gaba kadan.