Sama da ma’aikatan cibiyoyin Tarayyar Turai 100 ne suka hallara a Brussels a wata zanga-zangar adawa da yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza.
Masu zanga-zangar sun ajiye fararen ƙyallaye uku masu nuna alamar likkafani da jini a jikinsu a dandalin da ke wajen babban ofishin hukumar Tarayyar Turai da ke Brussels babban birnin Belgium.
A jikin ƙyallayen an rubuta kalmomin dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar EU da yarjejeniyar kisan kare dangi, a wani mataki na nuna rashin amincewa da yadda Isra’ila ta mayar da martani ga hare-haren da kungiyoyin gwagwarmaya karkashin jagorancin Hamas suka kai a ranar 7 ga Oktoba.
Wani ma’aikacin Hukumar Tarayyar Turai Manus Carlisle ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa “Muna wani taro na lumana, domin tsayawa tsayin daka wajen kare hakki da ka’idoji da ƙimar da cibiyoyin Turai suka ginu akai.”
Tawagar likitocin Falasdinu sun gano wani kabarin bai-ɗaya na uku a asibitin al-Shifa da ke Gaza, kamar yadda ofishin yada labaran gwamnatin kasar ya sanar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, ya zuwa yanzu an tono gawarwakin mutane 49 daga cikin kabari, kuma ana ci gaba da kokarin neman karin wasu.
Ofishin yada labaran ya ce an gano kaburbura guda uku a asibitin al-Shifa, uku a asibitin Nasser da ke kudancin birnin Khan Younis, da kuma daya a cikin asibitin Kamel Adwan da ke arewacin Gaza.
“Akalla gawarwakin mutane 520 ne aka tono daga cikin kaburburan bai-ɗaya bakwai,” in ji sanarwar.
Aƙalla Falasɗinawa 35 Isra’ila ta kashe da raunata wasu 129 a yayin wani mummunan hari da ta kai Rafah a sa’o’i 24 da suka wuce.
Sojojin sun kashe mutanen ne ta hanyar amfani da jirgin sama domin yi musu luguden wuta.
DUBA NAN: Halin Da Falasdinawa Zasu Shiga Idan Isra’ila Ta Kai Hari Rafah
Majiyoyi na ɓangaren kiwon lafiya sun ce Falasɗinawa da aka kashe ƴan gudun hijira ne waɗanda ba su jima da zuwa asibitin Kuwait ba da ke Rafah, inda majiyar ta ce akwai yara da mata a cikinsu.