Brazil Tana Bukatar Ton 750,000 Na Alkama Daga Iran.
Ministan ayyukan noma da kiwo na kasar Brazil wacce take ziyarar aiki a nan Tehran ta bayyana cewa kasarta tana bukatar kara yawan kayakin da take shigo da su daga kasar Iran, sannan daga ciki akwai alkama.
Kamfanin dillancin labaran Iranpress IP na kasar Iran ya nakalto Tereza Cristina tana fadar haka a nan birnin Tehran. Ta kuma kara da cewa. Brazil na bukatar ton 750,000 na alkama wanda idan Iran tana da shi zata saya.
Ministan ta kara da cewa a halin yanzu Brizil tana sayan takin zamani samfurin Urea daga kasar Iran wanda yake da mutukar muhimmanci wajen kyautata ayyukan noma a kasarta Brazil.
Daga karshen ministan ta ce ta zo kasar Iran ne don kara karfafa dankon zumuncin da tsakanin kasashen biyu, da kuma fadawa Tehran kan cewa ba ta ba da wani muhimmanci ga takunkuman da Amurka ta dorawa kasar ba.