Gwamnatin Brazil tace adadin mutanen da suka mutu sakamakon ruwan saman da aka shatata makon jiya ya kai 79, yayin da wasu da dama suka bata.
Ministan kula da ci gaban yankunan kasar ta brazil Daniel Ferreira ya shaidawa manema labarai cewar alkaluman da suka tattara sun tabbatar da mutuwar mutane 79.
Fereira yace, mutane da dama sun bace, kuma wasu 25 sun samu raunuka, yayin da 3,957 suka rasa muhallan su.
Ministan yayi gargadin cewar suna fuskantar Karin ruwan sama a yankin, saboda haka aka bukaci mutane su zauna cikin shirin ko ta kwana.
Wannan dai shi ne iftila’i na baya bayan nan a cikin jerin bala’o’i da suka hada da zabtarewar kasa da ambaliyar ruwa da suka haifar da matsanancin yanayi.
A wani labarin na daban masu aikin ceto a Brazil na cigaba da neman masu sauran rai cikin laka da baraguzan gine-gine, biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa, da zabtarewar kasa a birnin Petropolis, a daidai lokacin da kawo yanzu adadin wadanda suka mutu a iftila’in ya karu zuwa mutane 117
Har yanzu dai jami’an ceto na lalauben gwamman mutanen da suka bace, yayin da kuma ake fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu.
Guguwar dai ita ce ta baya bayan nan da ta afkawa Brazil cikin watanni ukun da suka gabata, masifun da masana suka ce sauyin yanayi ne ke kara ta’azzara su.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta Petropolis ta ce an ceto akalla mutane 24 da ransu.
Da farko an ce, ana fargabar kimanin mutane 300 sun bace sakamakon wannan ibtila’in na ranar Taklatar nan.
Masana sun bayyana cewa, ruwan da aka tafka na tsawon sa’o’i uku, yawansa ya yi daidai da ruwan sama na tsawon wata guda.