Firaministan Birtaniya Boris Johnson zai zaburar da shugabannin kasashen G7 a taronsu na wannan makon, domin ganin sun mayar da hankali kan yi wa daukacin al’ummar duniya allurar rigakafin Coronavirus nan da shekarar 2022.
A ranar Juma’a mai zuwa ne Birtaniya za ta karbi bakwancin taron kasashen G7 mafiya karfin tattalin arziki a duniya a lardin Cornwall da ke yankin kudu maso yammacin Ingila, taron da zai samu halartar Faransa da Italiya da Japan da Jamus da Amurka da kuma Canada.
Allurar rigakafin korona
Ana sa ran a wannan taro, Firaministan Birtaniya Boris Johnson zai yi kira ga shugabannin gungun G7 da su yi kyakkyawar dukufa wajen yi wa daukacin mutanen duniya rigakafin Covid-19 nan da karshen shekarar 2022 kamar yadda sanarwar fadar Dowing Street ta bayyana.
Mista Boris ya ce, yi wa daukacin duniya wannan rigakafin, zai kasance wani gagarumin dungulallen ci gaba da aka samu a tarihin harka lafiya.
Firaminiatsn ya kara da cewa, duniya ta zura musu ido don ganin yadda za su tunkari kalubale mafi girma da ya kunno kai tun bayan kawo karshen yaki, yana mai jaddada aniyar shawo kan annobar coronavirus.
AstraZaneca
Fadar Downing Street ta yi karin haske kan nasarorin da gwamnatin Birtaniya ta samu wajen goyon bayan kera rigakafin AstraZaneca tare da baza shi a sassan duniya.
Kazalika fadar ta bayyana irin goyon bayan da Birtaniya ta bai wa shirin Covax na samar da allurar rigakafin kyauta ga kasashe matalauta.
Amma sai dai akasarin mutanen kasashen duniya basu yadda da sahihancin allurar da covid 19 ba, labarai mabambanta suna ta yawo tsakanin al’ummar kasashen duniya wanda yake sanya shakku gami da alamun rashin yarda da allurar rigakafin ta korona a zukatan al’umma.
Abu mafi muhimmanci da masu sharhi suke tuhumar boris johnson dashio shine, me yasa ba zai damu da halin da kasar sa ta ingila take ciki ba wacce yanzu cutar ta korona ke cin karen ta babu babbaka kuma gwamnatin sa ta kasa komi a kai.