Babban jami’in diflomasiyyar amurka kuma sakataren gwamnatin kasar, antony blinken a lokacin daya bayyana gaban kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dokokin kasar amurka ya tabbatar da cewa amurkan ta sha kaye a afghanistan sakamakon fitar da tayi kuma cikin kankanin lokacin kungiyar taliban ta karbe madafun iko.
Antony blinken ya tabbatarwa da majalisar cewa, duk da kayen da suka sha a afghnistan din amma hakan bazai haka su cigaba da taimakawa amurkan da suke a afghanistan din ba kuma ma zasu cigaba da taimakon ‘yan afghanistan wadanda suke da alaka mai kyau dasu, hakan kuma na nufin a kwai yiwuwar su kwaso su daga afgnistan din idan bukatar hakan ta taso.
Gwamantin joe biden ta jam’iyyar democrat dai na shan suka daga abokan hamayya, inda a bangaren guda kuma jami’an gwamnatin ke kokarin kare kuskuren da suka tafka na barin afghanistan da kuma sallama ta a hannun kungiyar taliban. bayan shekaru ashirin da amurkan tayi tana asasrar dukiya da dakarun ta a wannan dadadden yaki wanda yaci miliyoyin daloli kuma maurkawa dubbai suka mutu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa blinken zai kuma bayyana a gaban ‘yan majalisa a fadar ”white house” domin kare gwamnatin joe biden bisa kayen da amurka ta sha yakin afghanistan kuma ya tabbatarwa da ‘yan majalisar cewa, babu laifin gwamnatin biden din wannan abin kunya da ya faru da amurkan.
Debe sauran dakarun amurkan da suka rage a afghanisran da kuma masu goyon bayan amurkan daga afghanistan na daga cikin sukan da mista blinken ya fuskanta amma a kokarin sa na kare kai mista blinken ya bayyana cewa mun gaji wa’adi ne amma bamu gaji tsari a daga gwamanatin data shude.
Ficewar amurka daga afghanistan bisa jagorancin joe biden wanda yayi sanadin dawowar taliban kan madafun iko ya janyo cece kuce tsakanin amurkawa wanda ana iya gane hakan yadda ‘yan majalisun amurkan suke numfarfashi kuma suna zargin juna bisa hakan.