Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya kai ziyara Morocco domin tattauna batun tsaron yankin, yayin da kuma zai gana da Yarima na Hadaddiyar Daular Larabawa Mohammed bin Zayed al-Nahyan.
Kafin ganawarsa da Firaministan Moroco Aziz Akhannouch, Blinken ya yi wata ganawa da Ministan Harkokin Wajen kasar Nasser Bourita akan abin da ya shafi tsaro ciki harda yaki da kungiyar IS da kuma Al-Qaida.
A daren yau ne ake kuma saran Blinken zai gana da Yarima Mohammed bin Zayed al-Nahyan a gidansa da ke Moroco wacce ke zuwa a kokarin da Amurka ke yi na farfado da dadaddiyar alakar dake tsakanin su.
A wani labarin na daban kuma Kungiyar Taliban ta umarci kamfanonin jiragen saman Kasar Afghanistan da su dakatar da yin bulaguro da matan da basa tare da muharramansu.
Jami’an Ma’aikatar sufurin jiragen saman Kasar sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa kungiyar ta dauki matakin ne bayan kammala tattaunawa ta musamman cikin makon da ya gabata tsakanin wakilanta da hukumar shige da fice dake birnin kabul, da kuma hukumomin jiragen saman kasar.
Daukar matakin hana jiragen saman Afghanistan yin bulaguro da mata na daga cikin matakan da suka saba wa ka’idojin al’ummar kasar, wadda sabuwar gwamnatin ke yi tun bayan kwace mulki.
Ko a makon da ya gabata kungiyar ta haramtawa maza da mata ziyartar wuraren shakatawa lokaci guda, musamman wadanda ke babban birnin kasar.
Rufe makarantun mata, hana su ayyukan gwamnati, tare da tilasta musu sauya yanayin shigarsu, ya kasance tsatsaurar akida da Taliban ta dauka wajen tafiyar da Afghanistan, lamarin dake nuna sannu a hankali ana cigaba da ware mata a harkokin yau da kullum.