Blaise Compore Ya Nemi Gafarar Iyalai Da Alummar kasar kan Kisan Thomos Sankara.
A cikin wata wasika da kakakin gwamnatin kasar ya yada ta kafafen yada labarai na kasar ya nuna cewa tsohon shugaban kasar Blaise Compore ya nemi Gafarar iyalan thomos Sankara da ma alummar kasar baki daya game da kisan tsohon shugaban kasar da kuma dukkan laifukan day a tafka a lokacin mulkinsa
Sai dai dama daga cikin Alummar kasar sun shiga cikin rudani game da sahihanci da kuma gaskiyar tsohon shugaban kasar kan wannan kalamai da yayi, na neman gafarar Alummar kasar.
Kamar yadda yazo acikin wasikar da kakakin gwamnatin kasar Lionel Bilgo ya karanta ta kafafen yada labarai na kasar cewa ina neman gafarar alummar kasar game da duk wani laifu da na aikata a lokacin mulkinsa musamman kuma iyalan dan uwana kuma abokina Thomos Sankara game da kisan gillan da aka yi masa
Compore ya mulki kasar ne sakamkon juyin mulki da yayi a shekara ta 1987 inda aka harfe shugaban kasar wancan lokacin thomos sankara da wasu mukarrabansa, kisan nasa ya kasance wani abu da ya dauki hankalin na tsawon shekaru 27 , a baya bayan nan ne wata koto a kasar ta yanke hukumcin daurin rai da rai kan Compore saboda hannu da yake dashi wani kisan sankara.