Gwamnatin Birtaniya ta taya zababben shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu murna bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.
Kasar Birtaniya ta aike da wannan sakon taya murnar ne ta hannun sakataren harkokin wajen kasar James Cleverly, duk da cewa ta yi kira ga mahukuntan Nijeriya da su yi la’akari kan koken jam’iyyun adawa da suka gabatar kan zaben, wanda ya fuskanci kalubale na na’ura kamar yadda masu sa ido na kasa da kasa da kungiyoyin farar hula suka yi nuni da shi.
James Cleverly ya ce: “Birtaniya ta yaba wa masu kada kuri’a ‘yan Nijeriya kan yadda suka fito don kada kuri’arsu a zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki ta tarayya sannan kuma suka yi hakuri da juriya wajen tabbatar da ‘yancinsu na dimokuradiyya, muna taya zababben shugaban kasa, Sanata Bola Ahmed Tinubu murna.”
“Mun ji koken jam’iyyun adawa kan sakamakon zaben da kuma damuwar da tawagogin sa ido da kungiyoyin farar hula suka bayyana game da kalubalen da aka fuskanta wanda suka hada da samun tsaiko da kalubalen na’urar zaben.
“Muna karfafawa hukumomi guiwa da su binciki duk wata damuwa kuma su dauki matakin warware koken da aka gabatar sannan kuma a mai da hankali kan baiwa al’ummar Nijeriya zabinsu”
Source:LeadershipHausa