An dakatar da cinikin kungiyar Chelsea kamar dai yada mammalakin wannan kungiya dan kasar Rasha Abramovich ya bukaci a yi a baya.Daukar wannan mataki daga gwamnatin Birtaniya na zuwa ne bayan da hukumomin suka dau wasu sabin takunkumai sanadiyyar yaki da ya barke tsakanin Rasha da Ukraine.
Tun bayan da Rasha ta kaddamar da wannan mamaya zuwa Ukraine, mammalakin wannan kungiya ta Chelsea duk da nuna damuwar sa a kai, Abramovich dan shekaru 55 babu sunan sa daga cikin mutanen da suka fuskanci wata barrazana daga kasashen Duniya.
Soke batun cinikin wannan kungiya ta Chelsea da gwamnatin Birtaniya ta yi na zuwa a wani lokaci da Rasha duk da zaman tattaunawa da aka soma,na saka attajirin Abramovich cikin wani yanayi marar kyau,duk da cewa gwamnatin Birtaniya ta sanar da daukar wasu jerryn matakai na yin sassauci ga kungiyar ta Chelsea tare da bata damar ci gaba da taka tamola a fagen gasar ta Frimiya ta Ingial.
A karshe yanzu kam kungiyar ta Chelsea na fatan shiga tattaunawa da hukumomin Birtaniya don ganin an cimma mafita a kan wannan matsalla.