Birtaniya ta ci tarar bankin GT dala miliyan 9.3 saboda gazawa a tsare-tsarensa
Hukumar da ke sa ido kan hada-hadar kuɗi ta Birtaniya ta ci tarar bankin GT dala miliyan 9.3 saboda gazawa a tsare-tsarensa na magance matsalar almundahanar kuɗaɗe.
A wata sanarwa da hukuma ta fitar, ta ce bankin ya gaza a tsarinsa na hana almundahanar kuɗi.
Kamfanin dillacin labari na Reuters ya ruwaito hukumar na cewa bankin ya kasa ɗaukar matakan da suka dace domin magance tsare-tsaren kare almundahanar kuɗaɗe, duk kuwa da irin gargaɗin da aka sha yi masa.
“Bankin da kansa ya gano irin tarin matsalolin da gazawar ke haifarwa, haka mu ma hukumarmu, amma duk da haka bankin bai ɗauki matakan da suka dace ba” kamar yadda sanarwar hukumar hada-hadar kuɗin ƙasar ta bayyana.
Haka kuma hukumar ta ce bankin bai ƙaryata gazawarsa da hukumar ta gano ba, sannan kuma ya amince zai biya tarar.
A wata sanarwa da bankin ya fitar, ya ce ya sasanta da hukumar hada-hadar kuɗin, ya kuma amince da abin da hukumar ta gano na gazawarsa tsakanin watan Oktoban 2014 zuwa Yulin 2019.
Sannan kuma ya amince zai biya tarar kamar yadda hukumar ta buƙata.
Read More :
Mutum shida sun jikkata a harin tashar jirgin ƙasa a birnin Paris.