Masu fafutukar wajen nuna adawa da manufofin gwamnatin Birtaniya na tura bakin haure zuwa Rwanda sun ce za su daukaka karar su zuwa kotun daukaka kara a litinin din nan.
Hakan na zuwa ne bayan da babbar kotun kasar ta ce jirgin farko dauke da masu neman mafaka kimanin 31 daga Birtaniya zai nufi kasar Rwanda ranar Talata, kafin wasu su bi sahu daga bisani.
Sai dai masu fafutukar da suka shigar da karar ta farko a babbar kotun, sun ce sun damu matuka kan halin da mutanen da aka shirya tilasta maida su gida zasu shiga don haka su ke kokarin hana tashin jirgin na farko.
Da yake magana a babban kotun a ranar Juma’a, Justice Swift ya ce bayyi la’akari da akwai wata hujja da zai sanya a ki kulada masu neman mafaka ba.
Sai dai ya ce za a sake nazarin shari’ar, inda babbar kotun za ta saurari daukaka karar manufar baki daya, kafin karshen watan Yuli.
Kamun da ‘yan sandar filin sauka da tashin jiragen saman Heathrow na birnin London na kasar A wani labarin na daban birtaniya su ka yi wa shugaban hukumar leken asirin kasar Rwanda Janar Emmanuel Karenzi Karake, dake kan sammacin kungiyar tarayyar Turai ya haifar kakkausar suka daga gwamnatin Kigali
Shi dai Janar Emmanuel Karenzi Karake, dan shekaru 54 a duniya a ranar assabar da ta gabata ne ‘yan sandan Interpol na kasar Britaniya suka kama shi da misalin karfe 9h45 na safiyar ranar assabar da ta gabata a filin sauka da tashin jiragen saman Heathrow dake birnin London, kamar yadda kakakin hukumar yan sanda ta Scotland Yard ya sanar.
Ya kuma kara da cewa, an kama shi ne karkashin sammacin da Kungiyar Tarayyar Turai, ta hannun mahukumtan kasar Spain ta gabatar ne, dangane da zarginsa da aikata laifukan yaki kan fararen hula a kasar Rwanda.
Sai dai kuma wata majiyar shara’a daga birnin Madrid na Spain ta ce, a halin yanzu ba a tuhumar Janar Karenzi Karake kan zargin aikata laifukan yaki, ana zargin sa ne, a kan ayyukan ta’addanci.
Tuni dai ministan harakokin wajen kasar ta Rwanda Uwargida Louise Mushikiwabo ta rubuta rashin amincewar kasarta da kamun, a shafinta na twitter.
A nasa bangaren ministan shara’ar kasar ta Rwanda Busingye Johnston ya soke wata ziyarar aiki da yayi niyar kaiwa a kasar Spain, inda ya yi niyar ganawa da takwaransa Rafael Catala, kamar yadda majiyar hukumomin Spain ta sanar.
Tun shekara ta 2008 kotun kasar Spain ke bincike kan aikata laifukan yaki, da na kisan kare dangi, tare da ta’addanci da aka aikata a Rwanda, inda a karkashin haka ta bada sammacin kama mata manyan jami’an gwamnatin Rwanda 40 da suka hada da Janar Emmanuel Karenzi Karake.