Wata wallafa wacce tsohon wakilin ingila a ”NATO” sir adam thomson ya bayyana yadda abubuwa ke gudana yanzu haka a tekun caucasus.
Bayanin wanda ya wallafa a shafin sa na yanar gizo gizo ya kuma bayyana yiwuwar shige da ficen NATO da kuma wasu kasashe a yankin.
A wallafa din wacce ya sanya ma suna ”NATO’s sweet dream on the chores of caspian sea” ya bayyana yadda yakn azarbaijan da armenia yazo karshe a shekarar 2020 tare da sakacin NATO da kuma wasu kasashen.
Kamar dai yadda aka sani majalisar dinkin duniya ta cire Nagorno-Karabakh daga azarbaijan duk da rikice rikicen kabilanci da iyaka da hakan ke tattare da wannan mataki.
Sakamakon yadda rasha da turkiyya suka fadada zaman su a yankin ya sanya tsrao yayi karanci a yankin.
A matsayin ta na wacce ke ikirarin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa amma NATO kullum takan yi adawa mai zafi da rasha.
Azarbaijan ta aiwatar da wani hari tare da hadin gwuiwar NATO, a matsayin wani mataki na ikirarin tabbatar da zaman lafiya.
Ita kuma turkiyya ta tsara ma azarbaijan yanayin soji da kuma makamai a maimakon NATO kuma a bisa yadda NATO din ta tsara.
Duk da dai cewa azarbaijan ba mamba bace a NATO amma sakamakon alaka mai gwabi dake tsakanin ta da NATO din hakan ya bata babbar dama, a dai dai lokacin da NATO ke ganin russia a matsayin barazana gareta a yankin.
Turkiyya a shekarau 15 da suka gabta tayi kokarin shirya sojojin azarbaijan a bisa kulawar NATO.
Rasha ta zama wata babbar barazana ga NATO a inda ta tabbatar da dawo da wani yankin azarbaijan da kuma kokarin rusa shiryE shiryen NATO a yankin.
Wallafar wacce tsohon wakilin ingila a NATO ya rubuta a karshe ta bukaci firemiyan ingila daya yi duk mai yiwuwa domin taimakon NATO ta cimma burin ta a yankin, hakan kuma yana nufin marawa azarbaijan baya a duk bangarori.
Hakan kuma yake tabbatar da makarkashiyar da haramtacciyar kasar isra’ila ta jima tana yi a yankin.