Bin Salman: Saudiyya Tana Cutar Damu Ta Bayan Fage
Dubai tayi nasarar hada sojoji ta hanyar kashe makudan kudade kuma sojojin sun ta’allaqu da su ne, sa’annan sunyi amfani da wadannan sojojin sun mamaye wasu yankuna na Yemen wanda ya hada da Adan. Bin
Sai dai bangaren Saudiyya basu iya samar da irin wannan abu ba, sai dai ‘yan bindigar Ikhwani da suka samar wadanda tsawon shekaru 9 suke yaki tare da su, kuma suna hakan ne sakamakon amfanuwar su gabadaya.
Amma dangane da kokarin Dubai na mamayar yankin Almehreh, da Hadr Maut, da kuma kokarin raba madatsar makha, a yankin Ta’az ta hanyar jingina da Muhammad bin Salih, Saudiyyawa suna ganin hakan kokarin zagaye su ne.
A bangare guda kuma Bin Za’id yana ta kokarin kawo cikas a alakar Saudiyya da Amurka, ko a wayar da Biden yayi da shi watannin da suka gabata yayi kokarin kambama shi maimakon bin Salman.
Read More: Saudiyya ce kan gaba wajen siyan hatsin Rasha
Wadannan lamurra ko guda daya fita a kwakwalwar mai jiran gadon Saudiyya Muhammad bin Salman ba wanda yake da manyan burika a gaba.
Daya daga cikin dalilan da yasa ya gaggauta shiryawa da Iran shine wannan sabani tsakanin sa da hadaddiyar daular larabawa, da kuma shirin da yake da shi a kan Bn Za’id.
Bin Salman ya sani sarai cewa Iran ce ta taimakawa Qatar bata sallamawa abinda yake so shi da tsohon mai jiran gadon Hadaddiyar daular larabawa ba, saboda haka yanzu idan yana so yayi wani shiri domin tunkarar Hadaddiyar daular larabawa yana bukatar taimakawa Iran.
Mutanen Hadaddiyar daular larabawa larabawa da a zahiri suke girmama Iran amma a bayan fage suna aiki ne domin cutar da Iran, wannan ya bawa Bin Salman fata domin tabbatar da Iran a tare da shi.
Dangane da yawan sabanin da ke tsakanin Hadaddiyar daular larabawa da Saudiyya jaridar Amurka “Wall Street Journal” tayi sharhi mai tsaho dangane da sabanin dake tsakanin Bin Salman da da bin Za’id.