Fararen hula 3 ne aka kashe a harin da jiragen yakin Ukraine suka kai a yankin Bilgorod da ke kudu maso yammacin Rasha.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, Gwamnan Bilgorod Vyacheslav Gladkov ya ce wani jirgin saman Ukraine mara matuki ya jefa bam a kan titi kusa da wurin shakatawa na lafiya a kauyen Lavi, inda ya kashe fararen hula uku.
Kauyen Lavi yana da tazarar kilomita 22 daga iyakar Rasha da Ukraine.
Har ila yau, an kai wani harin da wani jirgi mara matuki a safiyar yau Laraba, sa’o’i bayan harin makaman roka na Rasha a wasu kauyuka biyu da ke kusa da birnin Liman a gabashin Ukraine, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku, biyu kuma suka jikkata.
Bayan da hukumomin Rasha suka sanar da cewa sun harbo jirage marasa matuka da suka yi yunkurin kai hari a birnin Moscow da safiyar Laraba, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya ce Washington ba ta karfafa ko ba da damar kai hari a kasar Rasha.
Source:ABNA