Ranar Lahadi aka yi bikin ranar ma’aikata ta duniya, wanda aka saba gudanarwa a duk ranar 1 ga watan Mayu a kasashe daban daban.
Dubun dubatar masu zanga-zanga a sassan duniya sun mamaye tituna don bikin wannan rana, tare da matsa lamba ga hukumomi wajen ganin sun inganta ‘yancin ma’aikata.
Hotunan da ke yawo a kafafen yanar gizo sun nuna yadda dubban mutane suka yi gangami a kasar Sri Lanka, da Turkiyya, da India da Pakistan, har ma da Girka, da Faransa da dai sauran kasashe da dama.
Jama’a da kungiyoyin kwadago a biranen nahiyar Turai sun fito kan tituna domin gudanar da jerin gwano tare da sakonnin bukatu ga gwamnatocin su a wajen bikin ranar ma’aikatan, musamman a kasar Faransa inda aka yi amfani da hutun na karrama ma’aikata a matsayin lokacin gangamin nuna adawa da sabon shugaban kasar Emmanuel Macron da ya sake lashe zabe.
A Turkiya, ‘yan sandan kwantar da tarzoma sun kame masu zanga-zangar da dama da suke kokarin isa dandalin Taksim na Istanbul don gudanar da gangamin nuna adawa da matsalar tattalin arziki da hauhawar farashin kaya ya haifar.
A wani labarin na daban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana bukatar tsagaita wuta a yankin Ukraine domin rage radadin illar yakin ga jama’ar kasar da kuma na duniya baki daya. Guterres ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da Sakataren Harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov a birnin Moscow
Yace “Na san cewa ayau muna fuskantar matsaloli masu sarkakiya a Ukraine, da kuma fassara abinda ke faruwa ta fuskoki daban daban, akan assalin abinda ke faruwa a Ukraine”.
Guterres ya kara da cewa, Matakin bai kai ga dakile fatar samun tattaunawa ta hakika akan hanyar da tafi dacewa a bi domin takaita radadin da jama’a ke fuskanta ba.
A daya bangaren, Sakatare Janar din ya nuna matukar bukatar neman hanyoyin da zasu samar da shirin tatatunawa, da samar da yanayin shirin tsagaita wuta a cikin gaggawa da kuma samar da hanyar kawo zaman lafiya mai dorewa.
Yace, “Kuma akan wannan hanyar muna son yin duk abinda ya dace domin takaita illar yakin a kowane sashe na duniya”.