Shugaba Joe Biden na Amurka na shirin kai ziyara Poland a juma’a mai zuwa inda gana da shugaba Andrzej Duda don tattaunawa kan mamayar Rasha a Ukraine.
A cewar sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin fadar White House Jen Psaki ta ce Biden zai gana shugabancin NATO da na G7 da kuma EU gabanin ziyarar a Poland, don tattauna yadda za su bullowa Rasha a abin da ya kira zaluncin da ta ke aikatawa a Ukraine.
Psaki ta ce za su ci gaba da jan hankalin Duniya don ganin sun ci gaba da samun goyon baya ga al’ummar Ukraine tare da sukar shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Sai dai Psaki ta ce ziyarar ta Biden ba ta da shirin kai shi zuwa Ukraine don ganewa idonsa yakin, sabanin shugabannin Poland da Czech da kuma Slovakia da suka je har Kyiv don ganewa idonsa yadda yakin ke gudana.
A wani labarin na daban Rundunar sojin Scandinavia ta sanar cewa wani jirgin sojin Amurka da ke atisaye cikin kungiyar tsaro ta NATO ya yi hatsari a kasar Norway, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dukkan sojojin Amurka hudu da ke cikinsa.
Kimanin jirage 200 da wasu jiragen ruwa 50 ne ke halartar atisayen, wanda za a ci gaba da gudanar shi har zuwa ranar 1 ga watan Afrilu.
Tun a yammacin ranar Jumma’a aka bada rahoton bacewar jirgin samfurin V-22B Osprey na rundunar sojojin ruwan Amurka a kudancin Bodo da ke arewacin Norway.