Shugaban Amurka Joe Biden ya gargadi takwaransa na China Xi Jinping a kan illolin taimaka wa Rasha a yakin da take da Ukraine, a yayin da Chinar har yanzu bata nuna alamun bin sahun sauran kasashen duniya wajen yin Allah wadai da Rasha ba.
Sanarwar Fadar gwamnatin Joe Biden na zuwa ne bayan ganawa ta sa’o’i biyu da shugabannin suka yi ta wayar tarho a jiya Juma’a.
Sai dai China ba ta bayyana takamammen matsayinta ba bayan ganawar, inda tashar talabijin kasar ta ruwaito shugaba Xi yana cewa, babu abin da wanna yaki zai tsainana wa kowa, ayayin da babu wani bayani a game da caccakar Rasha.
A wani labarin na daban Kotun Duniya da ke birnin Hague a Holland ta umarci Rasha ta gaggauta dakatar da mamayar da ta ke yi wa Ukraine, dai dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ita ma a bangare guda ke sake mika rokonta ga Rasha wajen ganin an kawo karshen yakin tare da warware rikicin ta lumana.
Hukuncin kotun wanda babu tabbacin ko Rasha za ta mutunta shi, na zuwa ne a dai dai lokacin da dakarun kasar ke ci gaba da yiwa manyan biranen Ukraine kawanya, hare-haren hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ke cewa zuwa yanzu ya hallaka fararen hula dubu 1 da 834.
Tuni Ukraine ta bayyana hukuncin na ICJ da gagarumar nasara yayinda ta sha alwashin ci gaba da matsa kaimi har zuwa lokacin da Rashan za ta janye tare da dawowar zaman lafiya a sassan Kiev da kewaye.
Majalisar dinkin Duniya ta ce zuwa yanzu fararen hula fiye da miliyan 3 ne suka yi kaura daga yankunan da Moscow ta yiwa mamaya don tsira da rayukansu daga hare-haren Sojin.
Mai shari’a Joan Donoghue da ya jagoranci zaman shari’ar na yammacin jiya laraba, ya bayyana kotun ta ICJ a matsayin fadar tabbatar da adalci yana mai nuna damuwa da yadda Rasha ke amfani da karfin Soji a rikicin maimakon warware shi ta ruwan sanyi.
Bayanai sun ce ICJ ta zartas da hukuncin ne ba tare da halartar wakilcin Rasha a zaman shari’ar ba.
Cikin hujjojin da Ukraine ta kafa wajen shigar da karar gaban kotu shi ne zargin Rasha da kokarin kisan kare dangi kwatankwacin na shekarar 1948 batun da tuni Moscow ta musanta yayin zaman sauraren shari’ar na ranakun 7 da 8 ga watan da muke ciki bisa cewa babu hujjar da ke tabbatar da zargin.
Rasha dai na ci gaba da nanata cewa, matakinta na amfani da Soji a Ukraine kokari na kare kanta daga barazanar tsaron da ta ke fuskanta daga makiyanta da kungiyar tsaro ta NATO.