Biden Ya Gargadi Bin Salman Game Da Sake Maimaita Wata Tabargaza Bayan Kisan Khashoggi.
Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da cewa ya yi magana kan batun kisan gillar da aka yi wa dan jaridar Saudiyya Jamal Khashoggi a ganawarsa da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman.
Bayan ganawar da yarima mai jiran gado na Saudiyya, a ranar jiya Juma’a, Biden ya ce “batun Khashoggi ya kasance kan gaba a ajandar ganawar tasu.”
Biden ya kara da cewa “abin da ya faru da Khashoggi ya yi muni, kuma na bayyana karara cewa idan wani abu makamancin haka ya sake faruwa, za su fuskanci martani.”
An kashe dan jaridan Saudiyya Jamal Khashoggi a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul a watan Oktoban 2018, abin da Saudiyyar ta musunta daga farko, kafin daga bisani ta amince da hakan bayan da komai ya bayyana a fili dangane da wannan batu.
A nasu bangaren, hukumomin leken asirin Amurka sun nuna cewa Yarima Mohammed bin Salman na da alaka kai tsaye da kisan dan jaridar.
Shugaban Amurka Joe Biden ya yi gargadi ga yarima mai jiran gado na Saudiyya, yayin da cibiyoyin kare hakkin bil’adama suka soki ziyarar da ya kai Saudiyya da kuma ganawarsa da Mohammed bin Salman da ke da hannu a kisan Khashoggi.
Da sanyin safiyar Juma’a ne shugaban kasar Amurka Joe Biden ya isa filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke birnin Jeddah, a wata ziyarar aiki da ya kai kasar Saudiyya daga Palastinu da Isra’ila ta mamaye, inda ya janye alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabensa na mayar da kasar Saudiyya a matsayin kasa saniyar ware.